Wannan lamarin dai ya faru ne da yammacin jiya, inda mahaifiyar marigayyar ta shaidawa wakilinmu cewar suna zaune suna hira bayan ta dora abincin dare sai ta ce bari ta je makota, fitar ta kenan bai fi minti 30 ba sai kawai ta jiyo ihu. Koda ta fito sai ta iske ta nufi gidan sai ta ga an taru, shigar ta ke da wuya sai ta ga ana sauko da gawar yarinyar maisuna Kadija.
Mutanan dai muzauna unguwar Dabo ne dake yankin Kurna a cikin birnin Kano.
Shi ma mahaifin yarinyar ya bayyana mana irin yadda ya ji da wannan ibtilai, inda ya ce su dai har yanzu ba su gano yadda wannan lamarin ya faru ba.
Tuni dai ‘yan sandan Rijiyar Lemo suka zo suka tafi da gawar zuwa asibiti domin yin bincike.