Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya sanar da ganin jaririn watan Ramadan na shekarar 2023 a wasu sassan Najeriya.
A jawabin da ya yi na sanarwar wanda aka sanya a shafin Facebook na kwamitin ganin watan, Sarkin Musulmin ya ce an ga watan ne bayan samun rahotanni daga shugabannin addinin Musulunci da ke wasu jihohin ƙasar.