An gano ƴan sanda biyu cikin guda huɗu da suka ɓace a jihar Benue 


Fatai Owoseni, Kwamishinan ƴan sandan jihar Benue

Ƴan sanda a jihar Benue sun ce an gano biyu daga cikin yan sandan kwantar da tarzoma da aka bayyana sun ɓace lokacin wani hari da aka kai musu a ƙauyen Azege dake ƙaramar hukumar Logo dake jihar,an gano su da ransu.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, ASP Moses Joel Yamu a wata sanarwa da yafitar a daren ranar Asabar yace huɗu daga cikin ƴan sandan ba a gansu lokacin da ayarinsu ya fuskanci ruwan wuta daga wasu ƴan bindiga bayan da suka dawo daga wani sintiri a ƙauyen Ayilamo.

Yamu ya ce ƴan sandan biyu da aka gano tuni suka haɗe da ƴan uwansu yayin da ake san ran gano ragowar ƴan sandan biyu.

Jihar Benue dai ta ɗade tana fama da rikicin manoma da makiyaya amma rikicin ya ƙara ƙamari tun bayan da jihar ta fara aiwatar da dokar hana kiwon dabbobi a fili 

You may also like