
Rundunar yan sandan jihar Ebonyi ta gano wasu abubuwan fashewaa wani wuri mallakin kungiyar IPOB dake fafutukar kafa kasar Biafra.
Sanarwar ta ce maboyar da aka gano bama-baman nan ne wurin hada bam mafi girma a yankin kudu maso gabas da aka gano.
Yankin kudu maso gabas ya jima na fama da hare-hare musamman kan hukumomin gwamnati da kuma mutane musamman da suka fito daga yankin arewa.