An gano gano gawar wani jami’in difilomasiyar Najeriya a gidansa dake Sudan


An samu gawar wani jami’in jakadancin Najeriya a gidansa dake Khartoum babban birnin kasar Sudan.

Wasu majiyoyin tsaro biyu sun tabbatar da mutuwar jami’in kana suka ce tuni aka kaddamar da bincike domin gano musabbabin mutuwarsa.

Ma’aikatar harkokin wajen kasarnan ta bayyana jami’in da ya mutu da suna,Habibu Almu dake aiki da hukumar kula da shige da fice ta Najeriya a ofishin jakadancin kasarnan dake Sudan.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen, Elias Fatile,yafitar ya ce ma’aikatar ta kadu matuka da mutuwar jami’in ya kara da cewa suna jira rahoto daga ofishin jakadancin.

Amma kuma kamfanin Dillancin Labarai na Rueters ya ce gidan talabijin na Alarabiya ya bayyana cewa kisan gilla aka yiwa jami’in difilomasiyar.

You may also like