Yan Najeriya su uku aka gano sun mutu a gidansu dake yankin Uttam Nagar na birnin New Delhi dake kasar India.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya jiwo daga jaridar The Hindu cewa an gano gawar mutanen uku ne a ranar Juma’a.
An ce yan sanda sun samu kwalaben giya da kuma na lemo a gidan.Dukkanin mutanen uku an samu bakunansu na dauke kumfa.
Shibesh Sing, mataimakin kwamishinan yan sanda ya ce mutanen sun hada da David Christopher, Greece Ben da kuma David I.
Ya yin da Greece ke zaune a hawa na uku na gidan hayar,David an ce na zaune ne a hawa na biyu David (I) kuma ya kama hayar gida ne a kusa da su sai dai yana yawan kai wa mutanen ziyara.
“Greece da Ben na dauke da takardar izinin shiga kasar dake nuna kasuwanci ne ya kai su, ” Sing ya ce.
Yan sandan sun samu korafi daga mai gidan inda ta ce tana jin wani wari da bata yarda dashi ba daga gidan.
Dukkanin ginin na dauke ne da mutane da suka fito daga nahiyar Afirka.
Lokacin da yan sanda suka fasa kofa sun samu gawar Greece da Ben a daki daya ya yin da gawar David ke wani daki na daban.
Daya daga cikin gawar ta fara rubewa babu wata alama dake nuna an shake mutanen ko kuma alamar jin ciwo a jikin mutanen a cewar Sing.
Tuni yan sanda suka dauke gawar ya zuwa asibitin Deen Dayal Upadhyay domin gano musabbabin mutuwarsu.