An gano haramataccen wurin yin rijistar zabe a jihar Kwara


Hukumar Zabe Ta Kasa INEC, a jihar Kwara ta gano wani haramataccen wurin yi wa mutane rijistar zabe dake Offa a karamar hukumar Offa dake jihar.

A wata sanarwa da hukumar tafitar mai dauke da sahannun sakatarenta, Paul Aster, hukumar ta ce wasu batagarin mutane suna yin haramtacciyar rijista a Offa, jihar Kwara.

Sanarwar ta ce mutanen suna amfani da manhajar kwamfuta ta Corel Draw wajen kwaikwayon katin zabe irin na hukumar.

Saboda haka hukumar ta shawarci jama’a da su je cibiyoyin da aka tanada domin a yi musu rijistar a shirin cigaba da yi wa masu kada kuri’a rijista da ake yi a ƙasa baki daya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like