An Gano Kawunan Mutane Guda Uku Da Suka Fara Rubewa Cikin Wani Gida A Jihar Osun  Garin Gbogana dake karamar hukumar Ayedede a jihar Osun ya shiga rudani bayan da aka gano rubabbun kawunan mutane uku a wani gida dake yankin. 

Kawunan mutane uku da kuma sauran sassan jikin dan adam aka gano a ginin mai daki hudu.

  An gano kawunan ne bayan da wani irin wari ya damu mutanen yankin hakan yasa suka shiga binciken gidan da warin yake fitowa. 

A karshe bayan da wasu matasa suka balla kofar gidan tare da kutsawa ciki, sun gano sassan jikin bil’adama a warwatse a harabar gidan.

Lamidi Abiyoye shine mazaunin gidan kuma tuni aka damka shi hannun jami’an tsaro. 

Kakakin rundunar yan sandan jihar Folasade Odoro, yace mutumin da aka kama yace shi mai bada maganin garfajiya ne. 

Odoro yace za’a binciki lamarin sosai, kana a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like