A kokarinsa na ganin ya farfado da hanyoyin bunkasa tattalin arziki don samun karin kudaden shiga, gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar na kokarin farfado da harkokin hako ma’adanai.
A wata sanarwa da muka samu daga mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan sadarwa, sanarwar ta ce a yanzu haka sama da ma’adanai 60 iri daban-daban ne aka gano akwai su a jihar.
Wani babban mai zuba jari daga kasar Sin Mista Lam Wing Ki Wilkins, ya ziyarci jihar, inda aka kai shi wasu wurare da aka gano wadannan ma’adanai kamar Kwalli, Dutse me kyalli, da dai sauransu.
Shugaban hukumar habaka harkokin saka jari na jihar Bauchi Alhaji Aminu Musa ne ya wakilci Gwamnan jihar, inda ya zagaya da masu saka jarin izuwa wuraren da aka gano ma’adanai din da suka hada da Gwaram, Futuk da kuna Gokaru da ke jihar.
Mista Lam Wing Ki Wilkins, ya bayyana ra’ayinsa na kulla alaka da gwamnatin jihar Bauchi don bunkasa harkokin tattalin arziki a jihar.