An Gano Wani Haramtaccen Wurin Sarrafa Makamai A Neja


Hukumar ‘yan sanda a jihar Neja ta bankado wata haramtacciyar masana’antar kera makamai a karamar hukumar Mashegu dake jihar.

An samu bindigu na musamman 110 da suka hada da kananun bindigu, bindigar gida samfurin AK 47 da bindiga mai sarrafa kanta da kuma alburusai masu yawa. Miyagun makamai Da yake jawabi ga manema labarai yayin gabatar da makaman, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Paul Dibbal, ya bayyana hukumar ta samu rahoton cewar wasu mutane na kera makamai, kuma suka bi sahu ta hanyar amfani da dabarun aiki har ta kai ga sun yi nasarar cafke wadanda ke gudanar da muguwar sana’ar.

Ya kara jaddada cewar hukumar ‘yan sanda na aiki da umarnin babban Sifeton hukumar, Ibrahim Idris, domin tabbatar da makamai sun bar hannun farar hula.

Ya shawarci duk wani mutum ko kungiya dake da makamai da su mika su hannun hukumar ‘yan sanda kafin wa’adin da hukumar ta diba ya kare, wanda daga nan duk wanda aka kama da mallakar makami ba bisa ka’ida ba zai fuskanci fushin hukuma.

You may also like