An Gano Wani Kabari Da Ciyawar Kansa Bata Bushewa Lokacin RaniWani abin al’ajabi ya auku a wata makabarta dake wata unguwa da ake kira Malleri, a cikin kwaryar birnin Sakkwato, a karamar hukumar mulkin Sakkwato ta Arewa inda aka gano wani kabari da ciyawar dake kansa ba ya mutuwa walau da rani ko da damina.

Wani makusanci da wannan makabarta mai suna Yusuf Abubakar Ahmad, ya bayyanawa RARIYA cewa ya taso tun yana karami, ya sami wannan kabarin wanda babu tabbacin namiji ko macce a haka, Wanda Allah yaba ni’imarsa a cikin iyawarsa, dausayin sanyi da ciyawa a samansa, kuma ciyawar ba ta mutuwa a rani, amma sauran fadin makabatar a rani tana bushewa, banda wannan kabarin.
Lokacin Damina babu wata kalar ciyawar dake fitowa saman kabarin, kuma ruwan damina bai sanya ciyawar ta wuce girman da take da shi a cikin rani, kuma dabbobi basa cin ciyawar kabarin, kabrukka makusanta kabarin za a ga sun nashe da sanyin da ya fito da wancen kabarin.

You may also like