An Gargadi Fulani Da Su Guji Daukan Doka A Hannunsu


Hukumar kula da al-amuran Fulani makiyaya da manoma ta jihar jigawa ta gargadi al-umma su guji daukan doka a hannun su.


Sakataren zartarwa na hukumar, Dakta Rabi`u Miko ne yayi gargadin a lokacin bada tallafi ga wadanda rikicin Fulani da makiyaya ya shafa a garin Marma na karamar hukumar Kiri-Kasamma.

Dokta Rabi,u Miko yayi bayanin cewa gwamnatin jiha na daukan matakan da suka kamata dan kawo karshen matsalar dake faruwa a tsakanin bangarorin biyu ta hanyar samar da makiyayu da burtulai da kuma shata kan iyakar gonakai.

Yace a wannan shekarar akwai tsare tsaren da aka tanada dan tabbatar da ganin ba,a sami wata matsala ba tsakanin bangarorin biyu.

Da yake raba tallafin ga wadanda iftila`in ya shafa, sakataren zartarwa na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, Alhaji Yusuf Sani Babura yace gwamnati ta bada talalfin ne domin rage musu radadin da suke fuskanta.

Ya kara da cewa gwamnatin jiha tana kokari wajen dakile rigingimu dake afkuwa tsakanin makiyaya da manoma ta hanyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin samo bakin zaren.

A nasa jawabin wakilin mazabar Kiri-Kasamma a majalisar dokokin jiha, Alhaji Aliyu Ahmad Madachi yace suna daukar matakan da zai kawo karshen matsalolin dake faruwa tsakanin makiyaya da manoma a jihar.

Daga nan yayi kira ga alummar yankin su zauna lafiya da junasu a kowane lokaci domin samun cigaba mai dorewa.

A jawabansu daban daban wadanda suka ci gajiyar tallafin sun bayyana godiya ga gwamnatin jiha kawo musu dauki cikin gaggawa.

You may also like