Rundunar ƴan sandan jihar Yobe tace ya zuwa yanzu jumullar ɗalibai 111 aka gaza gano inda suke a kwalejin fasaha ta ƴan mata dake Dapchi a jihar Yobe. Bayan harin da ƙungiyar Boko Haram ta kai makarantar a ranar Litinin.
Hakan na zuwa ne jim kadan bayan da kwamishinan ilimin jihar Muhammad Lamin ya ce ɗalibai 48 da suka ɓace sun dawo makarantar.
Lamin yace “hakan yasa yawan dalibai 94 da suka ɓace a daren jiya bayan ƙirgasu da aka yi ya dawo 48.har yanzu muna fata wasu da dama za su dawo nan da ɗan lokaci kaɗan.”
Amma Abdulmalik Sumonu kwamishinan ƴan sandan jihar ya musalta haka inda yace ɗalibai 111 ba 94 ba aka gaza gano inda suke.
Da yakewa ƴan jaridu jawabi ranar Talata a Damaturu babban birnin jihar Sumonu ya ce ” ɗalibai 815 cikin 926 aka iya gani a cikin makarantar a ranar Talata.
“Akwai rahotannin dake cewa ƴan mata da dama sun dawo makarantar bayan da aka ƙidaya ɗaliban.”
Kwamishinan ya ƙara da cewa babu rahoton samu asarar rayuka ko kuma sace ɗalibai a makarantar.