An Girke Ƴan Sanda 2000 a Makarantu 300 Na Jihohin Yobe Da Borno


Kimanin jami’an ‘yan sanda 2000 aka girke a makarantu kusan 300 da ke jihohin Borno, Yobe da Adamawa don tsaron lafiyar daliban da ke karatu a wadannan makarantun.

Shugaban Rundunar ‘yan sanda, Ibrahim Idiris ya ce an dauki wannan matakin ne don dakile duk wani sabon yunkuri na mayakan Boko Haram na kai hari a wata makaranta kamar yadda suka arce da daliban makarantan Sakandaren Dapchi kwanaki.

You may also like