An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Ga Shugaba Buhari A Jihar Taraba


A jihar Taraba an gudanar da addu’oi na masamman na zaman lafiya a Najeriya da kuma shugaba Muhammadu Buhari, da fatan Allah ya bashi lafiya.

Yayin taron addu’ar da Malamai da dama suka jagoranta an karanto Al-Qurani, da addu’o’i da kuma yin tawassuli da darajar wannan watan.

Ustaz Shuaibu Muhammad na kungiyar Izala wanda ya kasance daya daga cikin jagorori a wannan addu’ar, yace yiwa Najeriya da shugabanta addu’a ya zama wajibi domin ci gaban kasar da kuma samun walwala cikin wadata ga ‘yan kasar.

Alh.Adamu Tibanson Garkuwan Dakka ya kwatanta shugaba Buhari da jagoran canji da ya cancanci addu’a a wannan lokaci.

Yayin da wasu ke addu’o’i, wasu ko na ganin ana neman wuce makadi da rawa game da batun rashin lafiyar shugaban kasar ta hanyar neman siyasantar da batun.

Muhammad Ibrahim wani dan jarida a Najeriya na ganin wasu na neman bangarartar da batun rashin lafiyar shugaba Buhari abinda yace hakan bai dace ba.

Muhammad Ibrahim wanda ya caccaki malaman addini dake zakewa, yace kamata yayi a bar shugaba Buhari ya cigaba da jinya maimakon cewa dole ya cigaba da mulki.

Wannan ko na zuwa ne yayin da yan Najeriya ke haramar bukukuwan ranar demokaradiya a gobe littinin 29 ga watan Mayu.

You may also like