An Gudanar Da Bikin Takutuha A Kano



A jiya Litinin ne aka gudanar da bikin Takutuha kamar yadda aka saba duk shekara domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad S A W.

Ana yin bukunkuna kala-kala, wanda hakan ne ya sa matasa musamman mabiya Darikar Tijjaniyya da Kadiriyya ke halarta.
 


Shahararren Malamin nan Sharu Sani Janbulo shine yake jagoranta inda suke tasowa daga gidansa zuwa zagayan cikin birnin Kano domin nuna farin cikinsu. Ana yin bikin ne cikin kyakyawan tsaro.

You may also like