An Gudanar Da Muhimmin Taro Domin Shawo Kan Matsalar Tsaro a Yankin Arewa


A yau Laraba ne Gwamna Jihar Bauchi Barista Mohammed A. Abubakar ya halarci taron masu ruwa da tsaki na jihohin da suke yankin Arewa don tattauna batutuwa akan yadda za a hada karfi da karfe a shawo kan lamarin tsaro a yankin.

A yayin taron, Gwamna M.A Abubakar ne ya yi jawabi a madadin Gwamnonin Arewacin kasar nan. Inda Gwamna ya bayyana muhimmancin taron, ya kuma kara da cewa wannan taro ya zo daidai lokacin da ake bukata don dakile abubuwan dake barazana ga rayuwar mazauna yankin, musamman yadda aka tattaro duk wani mai ruwada tsaki zuwa wajen taron.

Taron wadda ya hada da Gwamnonin Jihohin Arewa, Sarakuna, masu fada aji akan sha’anin tsaro, tsoffin manyan Jami’an tsaro, Jami’an tsaron da suke aiki yanzu da dai sauran su, Shugaban ‘yan sandan Nijeriya Ibrahim Kpotun Idris ne ya shirya shi don samun matsaya ga harkar tsaro a Arewacin Nijeriya baki daya.

Mai Alfarma Sarkin Musulmai Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda shine shugaban taron, ya jinjina wa shugaban ‘yan sandan bisa hada irin wannan gagarumin taro da ya yi.

A karshen taron an gabatar da addu’o’i na neman samun zaman lafiya da dorewar zaman lafiya a wasu jihohi da suke zaune lafiya.

You may also like