An gudanar da taron addu’a kan ziyarar aiki da Buhari zai kai jihar Kano 


An gudanar da taron addu’a a masallacin juma’a dake fadar gwamnatin Kano bayan da aka kammala sallar juma’a, domin samun nasarar ziyarar aiki da shugaban kasa Muhammad Buhari zai kai jihar, ta kwanaki biyu daga ranar Laraba 6 ga watan Disamba.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na daga cikin wadanda da suka halarci taron addu’ar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Salihu Tanko Yakasai ya fitar yace yayin ziyarar shugaban ƙasa zai kaddamar da wasu aiyuka da gwamnatin jihar ta samar.

“Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya halarci sallar juma’ah a massalacin juma’a dake fadar gwamnatin Jihar Kano a yau.

“An gudanar da addu’o’i na mussaman bisa ziyarar aiki ta kwana 2 da Mai Girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kawo Jihar Kano daga ranar Laraba, 6 December 2017, domin kaddamar da manya manyan aiyukan a Jihar,” Yakasai yace.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like