Jam’iyar APC a jihar Katsina ta gudanar da gangamin taron zaben shuwagabannin Jam’iyar a matakin kananan hukumomi a fadin jihar a jiya Asabar.
Da yake karin haske yayin ziyarar gani da ido da ya kai wajen taron, jami’in yada labaran gidan Gwamnatin jihar Katsina Ibrahim Mu’azzam Abdullahi ya nuna gamsuwarsa ga yadda ya ga zaben na gudana ba tareda korafi ba.
Abdullahi ya kuma jijina wa masu zaben ganin yadda suka fito ba hayaniya kuma suka yarda aka yi sulhu tsakanin wasu ‘yan takarar, inda mataimakin Gwamnan jihar Mannir Yakubu da Shugaban Jam’iyar APC na Jaha Shitu Masalaha suka jagoranci zaben a cikin garin Katsina.
Sai kuma Shugaban Ma’aikata na gidan Gwamnati Alhaji Bello Mandiya da kuma Shugaban hukumar SEMA suka jagorancin zaben yankin Funtua da aka gudanar a Malumfashi, inda kwamishinan Shari’a Barr Ahmed El-marzouq ya jagoranci shiyyar yankin Daura.
A ranar asabar mai zuwa dai ake sa ran gudanar da zaben a matakin jiha wanda wadannan jami’an ne za su jagorancin Jam’iyar APC na tsawon shekaru hudu.