An gurfanar da Fulani 6 gaban kotu kan harin Benue


Yan’sanda a jihar Benue sun gurfanar da mutane shida da ake zargi Fulani makiyaya ne masu kashe-kashen mutanen da akeyi a kananan hukumomin Logo da Guma dake jihar.

Mutanen da ake zargin an gurfanar da su gaban babbar kotun majistire dake Makurdi babban birnin jihar a ranar juma’a.

Yan’sanda sun ce sun kama Fulani makiyaya  takwas, shida a Guma biyu a Logo   da ake zargi suna da hannu a kai harin.

Samuel Ortom gwamnan jihar yace harin ya jawo asarar rayukan mutane sama da   20  ciki har da mace mai juna biyu da kuma dabbobi guda bakwai.
Wasu da dama kuma suka jikkata inda suke karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Benue.

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya tabbatarwa da gwamnatin jihar da kuma mazauna jihar cewa ana ƙoƙarin gano wadanda suka aikata haka domin su fuskanci hukunci da kuma hana faruwar haka anan gaba.

You may also like