Matar nan da ake zargi da kashe mijinta, wato Maryam Sanda, ta bayyana a gaban wata babbar kotu a Abuja a yau Juma’a.
Lauya mai shigar da kara ya ce suna so su sauya tuhume-tuhume saboda sabbin hujjoji da aka samu sakamakon bincken da ake yi mata.
Maryam dai ta shiga kotun ne dauke da jaririyarta da kuma KURANI MAIGIRMA a hannunta,wanda hakan ke nuni da tsantsar nuna nadamar ta a fili inda ta lullube fuskarta ba a iya ganin fuskar kwata-kwata.
Sai muce Allah Ya Rabamu da aikata aikin da nasani.