An Gurfanar Da Wasu Masoya Bisa Gutserewa Wata Kunne



Rundunar ‘Yan sandan Legas ta maka wasu masoya biyu kotu bisa tuhumar gutserewa wata mata mai sayar da ruwan Leda kunne a unguwar Mushin da ke jihar.

Mai gabatar da kara a kotun Insfecto Rita Momoh ta  bayyana cewa masoyan, Mista Friday Aigbogun da budurwarsa, Olamide Fashanu sun tafi gidan matar wadda ke sayar da ruwan ledan mai suna Misis Ajoke Wasiu inda suka sayi na Naira talatin sannan suka nemi a saka masu a cikin bakin Leda.

Ta ci gaba da cewa, Misis Ajoke ta nuna wa masoyan cewa ba ta da irin wannan ledan, lamarin da ya harzuka su inda suka rika zaginta wanda a kan haka ta mayar da martani, lamarin da ya janyo Fada ya kaure a tsakaninsu wanda daga nan ne budurwar Mista Friday ta sa hakuri ta gutsere kunne Misis Ajoke. Masoyan dai suna fuskantar zaman kurkuku na tsawon shekaru bakwai inda har an same su da laifin da ake zarginsu.

You may also like