An Gurfanar da wasu ‘yan Hizbah a kotu


An gurfanar da wasu ‘yan Hizbah a gaban wata babbar kotun shari’ar musulunci bisa zargin gwada karfi a kan wasu ‘yan jarida biyu.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ce ta gurfanar da jami’an hukumar ta Hizbar uku inda ake tuhumar uku kan hada baki da bata-suna da kuma gwada karfi da cin zarafi ba bisa doka ba, ga Abdullahi Isah da Sa’adatu Yakubu Abdullahi.

A ranar Asabar da ta gabata ne dai aka lakadawa yan jaridar duka, lokacin wani taro don sauraron wani fitaccen makarancin litattafan Hausa a rediyo, Ahmad Isah Koko, taron da aka iyakance cewa na maza ne kawai.Sai dai, da aka karanto musu tuhumar a gaban mai shari’ah Garba Ahmad Ibrahim, ‘yan hizbar sun musanta aikata wani laifi.

Alkalin ya bayar da belinsu tare da dage shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Satumba.Lauyan wadanda ake kara, Barista Nabahani Usman ya ce hukumar ta Hizbah za ta yi kokarin neman sulhu saboda fahmitar junan da ke tsakaninta da ‘yan jarida.

Rundunar hizbah ta jihar Kano ta taba hana fitaccen makarancin littattafan gudanar da taro a baya, bisa zargin za a samu cudanya tsakanin maza da mata.

You may also like