An Gurfanar da Wasu Yan Uwa Biyu A Gaban kan Laifin Sace Yarinya Yar Shekara 14 Da Kuma Aikata Fyade  


Hakkin mallakar Hoto :Premium Times

Wani mutum dan shekara 28, Ifeanyi Nwaneze da kuma yar uwarsa  Ginika Ojukwu, wadanda ake zarginsu da hada baki tare da sace yarinya yar shekara 14, an gurfanar da su kotun Majistire ta Tinubu dake jihar legas.

 Mutun  na farko da ake zargi Nwaneze dake zaune a Titin Tapa dake Orile-Iganmu,ana kuma tuhumar sa da laifin yiwa yarinya yar shekara 14  fyade.

Mai gabatar da kara Ben Ekundayo ya fadawa kotun cewa  mutumin da ake zargi ya aikata laifin a ranar 16 ga Yuni  a Titin Adeniji Adele dake Legas. 
Mutumin da ake zargi ya sace yarinyar lokacin da take kan hanyarta ta zuwa masallaci. 

 A cewar Ekundayo mutumin da ake zargi ya tsare yarinyar a gidan yayarsa har tsawon kwanaki hudu ba tare da son ranta ba tare  da  yi mata fyade.

   “Mutumin da ake zargi ya tsare yarinyar a gidan Ojukwu har tsawon kwanaki hudu, alhalin tasan cewa dan uwanta garkuwa da yarinyar yayi.

  “Nwaneze ya aikata lalata da yarinyar ta karfin tsiya ,”yace. 

Laifukan da suka aikata ya saba da sashi na 127, 266 da kuma sashi na  409 na kundin dokar manyan laifuka ta jihar Legas.

  Mutanen biyu sun musalta zarge zargen da ake musu guda uku na, hada baki, sace mutum da kuma aikata fyade.

Kotun ta bada belin mutanen kan kudi Naira 500,000 kowannensu tare da mutanen daza su tsaya musu. 

An kuma daga shariar zuwa ranar 8 ga watan Yuni. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like