Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba na nuni da cewa an kashe mutane da dama a wani faɗa tsakanin fulani da kuma wasu ƙauyawa a ƙaramar hukumar song ta jihar Adamawa.
Rikicin da yafaru a ƙauyukan Simba da kuma Shure a ranar Juma’a ya jawo an lalata gidaje da dama.
Rikicin yafara ne lokacin da Fulani suka kai shanunsu shan ruwa a wata a korama wacce da ita mutanen ƙauyen suka dogara wajen samun ruwan sha.
Hakan ya jawo faɗa tsakanin ɗaya daga cikin mutanen ƙauyen da kuma makiyayan har ta kai ga ya samu rauni
Samun labarin abinda yafaru yasa ƴan kauyen suka kai hari kan makiyayan inda suka kashe da dama daga cikinsu.
Daga bisani makiyayan sun kaddamar da harin ɗaukar fansa kan ƙauyukan.
Waɗansu mutane ance sun rasa rayukansu a harin ɗaukar fansar ya yin da aka ƙona wasu gidaje.
Othman Abubakar,mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar Adamawa ya tabbatar da faruwar rikicin amma bai yi ƙarin haske ba akai.