An halaka mutane kusan 50 a Benue | Labarai | DWHarin da ya faru a ranar Laraba a ritsa ne da al’ummomin Umogidi da ke jihar Benue, inda ake yawan samun tashe-tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma da ke neman filaye da albarkatun kasa.

Mai baiwa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro Paul Hemba, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, an samu ceto gawarwakin mutane 46 daga cikin wadanda aka kashe, kuma har yanzu ba a san inda wasu suke ba.

Ya zargi makiyaya da kai harin, kamar yadda suka sha kai wa al’ummomin yankin a cikin watan da ya gabata. Ya zuwa yanzu dai ba a fayyace dalilin kai harin ba, amma Benue na daya daga cikin wuraren da rikicin manoma da makiyaya ya fi kamari a Najeriya.

 

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like