An hana kallon mata a indiya


Masu amfani da dandalin sada zumunta a India sun mayar da martani cikin mamaki da annashuwa, bayan wani babban jami’i ya ce ya saba doka namiji ya kalli mace fiye da dakika 14.

Babu wata doka game da hakan a kasar, amma kwamishinan haraji na jihar Kerala, Rishiraj Singh ya ce kallon kurulla zai iya sa wa a daure mutum.

Indiya na daya daga cikin kasashen kalilan na duniya damaza suka fi mata yawa.

Masu mu’amala da shafukan intanet sun dinga tambayar cewa me zai faru idan mutum ya kifta idonsa?Suna ba’a da cewa ta yiwu kudin bakin tabarau ya tashi.Wata daliba ta yi shagube da cewa za ta iya kai rahoto da dama a rana kan kallon kurullar da aka yi mata.

Ko da yake wasu shafukan intanet sun kare Mista Singha kan maganar da suke ganin ya yi ne domin kare mata.

You may also like