An Hana  Sarkin Zazzau Shiga Wurin Taro A Kaduna 


Sarkin Zazzau Mai Martaba Shehu Idiris ya fuskanci wulakanci lokacin da ya halarci wurin bikin bude sabon kamfanin samar da kananan kaji da kuma abincinsu da aka bude a Kaduna.

An dai kashe dalar Amurika miliyan 150 wajen samar da kamfanin kuma ana sa ran zai rika samar da kananan kaji  1200000 a duk  mako,  da kuma aiyukan yi 3000.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa sarkin ya is wurin taron a ranar Talata da safe mintuna kadan bayan zuwan gwamna Nasiru El-Rufai.

Duk da cewa babban bako shugaban kasa Muhammad Buhari bai iso wurin taron ba amma jamian tsaro sun hana sarkin na Zazzau da jama’arsa shiga wurin taron bisa umarnin da suka ce sun samu daga sama.

Shedun gani da ido sun ce sarkin ya shafe mintuna talatin yana jira kafin daga bisani ayi masa tayin shiga wurin taron shi kadai ba tare da yan tawagarsa ba. 

Sarkin dake cikin fushi yayi watsi da tayin da akayi masa inda yabar wurin taron a fusace.

“Yayin da suka hana sarkin Zazzau shiga wurin taron  Sarkin Kano dana Marwa sun zo daga baya amma aka barsu suka shiga wurin taron da tawagarsu.” shedar gani da idon yace.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like