An Haramta Karatun Diploma a Jami’o’in Najeriya


Hukumar da ke sa ido kan jami’oi ta Nijeriya, NUC, ta haramta karatun diploma da jami’o’in kasar nan ke bayarwa.
Hukumar ta ce duk da cewa jami’o’in sun kwashe shekara da shekaru suna yin hakan a wurinta sun sabawa ka’ida kuma karatun haramtacce ne.
Guraben karatu da jami’oin gwamnatin kasar ke samarwa dai sun yi karanci ga miliyoyin mutanen da ke bukatar karatu mai zurfi a kasar duk kuwa da cewa an samu yawaitar jami’o’i masu zaman kansu fiye da a baya a kasar.
Daraktan hulda da jama’a na hukumar ta NUC, Malam Ibrahim Usman Yakasai, ya gaya wa manema labarai cewa, in ban da diplomar da ake yi a jami’ar ABU, tun lokacin Frimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello, Sardauna, ba a yarda da duk ta wata jami’a ba.
Jami’in ya ce duk dalibin da yake son yin karatun diploma sai ya je kwalejojin kimiyya da fasaha (polytechnics), amma ba jami’a ba.

You may also like