An Haramta Koyar Da Turanci A Kasar IranIran ta haramta koyar da harshen Ingilishi a makarantun Firamare na kasar inda ta ce harshen na gurbata al’adu. Ma’aikatar ilimi ta kasar ta ce ta na fatan karfafa koyon harshen Farsi da kuma al’adun Musulunci na kasar ga daliban Firamare.

A kwanakin baya Jagoran addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya nuna damuwa kan yadda ake koyar da harshen Ingilishi.

You may also like