Kotun ladabtar da ‘yan wasa ta goyi bayan hukuncin dakatar da ‘yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Rasha daga shiga wasannin Olympics a Rio na Brazil.
Hukumar kula da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ce ta haramta wa ‘yan wasan Rasha shiga wasannin da za a fara a ranar 5 ga watan gobe.
Hukumar ta IAAF ta dauki matakin ne bayan wani rahoto ya bayyana yadda ‘yan wasan ke kwan-kwadan kwayoyin kara kuzari, lamarin da ake zargin hannun gwamnati a ciki.
Kotun ta goyi bayan dakatarwar ce a wannan Alhamis bayan ‘yan wasan na Rasha sun shigar da kara kan hukuncin da IAAF ta dauka a kan su.
A bangare guda, shi ma kwamitin wasannin Olympic na duniya na nazari kan batun haramta wa ilahirin ‘yan wasan Rasha shiga wasannin Olympics a Brazil.