An Haramtawa Dan Bilki Kwamanda Magana A Rediyo Sakamakon Cin Zarafin Sarkin Kano Dayayi. 



Addinin Musulunci Addini ne Wanda ya koyar Da Al’umma Da cewa Su Fadi Alkhairi Ko kuma suja Bakinsu suyi shiru,  Amma Shi Dan Bilki Kwamanda an bayyana shi da mutumin da baya sawa bakinsa linzami wajen yin magana,  a wannan dalilin ne Gidan Rediyon na FREEDOM ta Jihar kano Suka Haramta Masa Yin Magana na har abada. 

Ga kadan daga irin katobarar da ya taba fada


***Ba wanda na ke jin tsoro a cikin ku kuma babu wanda ba ni da sirrin sa…. (martanin sa ga IZALA) 
**In Allah Ya yarda buhun shinkafa sai ya kai N20,000 duk abinda talaka zai yi ya je yayi.. (martanin sa ga talakawa) 
**Ba ma son shawarar ka, kuma idan ka kara taba Buhari sai na yi maka Kaca-Kaca.. (martanin sa ga Sarkin Kano) 
Gidan Rediyo mafi farin jini a jihar Kano Freedom FM ya haramtawa Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda magana har abada. Wannan kuwa ya biyo baya ne sakamakon cin zarafin Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II da ya yi da sunan mayar da martani akan shawarar da ya ba wa shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari. 
Idan ba a manta ba a baya ya taba cin zarafin Malam Ibrahim Shekarau aka lakada masa dukan Kawo-wuka.

You may also like