An Haramtawa Malamin Saudiyya Wa’azi Saboda Ya Nemi Hana Mata Tukin MotaAn haramtawa wani shaihin malami yin wa’azi a Saudiyya sakamakon bayyana rashin dacewar barin mata su tuka mota, a inda ya bayyana hakan da shashanci.
A wani bidiyo da ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta, Sheikh Sa’ad al Hajari ya ce kaifin tunanin mata rabin na maza ne, kuma da zarar sun kammala cefane idan suka je kasuwa to aikin kwalkwalwar tasu na zama rubu’in na namiji.

You may also like