An harbe ma’aikatan NDLEA uku a jihar KogiMa’aikatan Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, NDLEA, uku aka harbe har lahira a Okene dake jihar Kogi.

Idris Bello, kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar Kogi, ya ce an harbe ma’aikatan ne lokacin da suke bakin aiki.

Ya ce an kashe su ne da misalin karfe 8:30 na daren ranar Asabar.

Bello ya ce yan bindigar sun zo ne a kafa kuma lamarin yafaru ne a dai-dai babbar kofar shiga kwalejin ilimi dake Okene.

Ya bayyana sunan jami’an hukumar da suka mutu da suka hada Nicholas Onwumere, Ebun Peters and Abdulrahman Musa.

Kwamandan ya kara da cewa ma’aikatan suna aikine tare da ragowar abokan aikinsu uku lokacin da maharan suka farmusu.

Ma’aikatan uku sun mutu a wurin nan take suka mutu yayin da ragowar suka tsira da ransu ba tare da ko kwarzane ba.

Ya ce yan bindigar sun dauke bindigogin jami’an da suka rasa ransu kafin su ranta a nakare.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like