An harbe sojan sama daya a wani hari kan wurin saukar jiragen masu saukar ungulu dake jihar Bayelsa


Wasu yan bindiga sun kai hari kan wurin saukar jirage masu saukar ungulu na Rundunar Sojin Saman Najeriya dake Igbodene a Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa.

Yan bindigar sun samu nasarar kashe sojan sama guda daya.

Olatakumbo Adesanya, Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar ya tabbatar da faruwar harin cikin wata sanarwa da ya fitar.

Yace ma’aikatan dake bakin aiki sun samu nasarar dakile harin duk da cewa sojan sama guda ya rasa ransa.

Adesanya ya kara da cewa, Sadique Abubakar, shugaban rundunar sojan saman Najeriya ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar harin.

Jihar Bayelsa na daya daga cikin jihohin Najeriya dake fama da matsalar rashin tsaro.

Makonni biyu da suka wuce sai da wasu yan bindiga suka kashe, Ebikimi Okoringa wani mai taimakawa gwamnan jihar Seriake Dickson.

You may also like