An harbe ‘yan sanda uku


 

Rahotanni daga jihar Louisiana da ke Amirka na cewar an hallaka wasu ‘yan sanda uku tare kuma da jikkata wasu guda uku a babban birnin jihar wato Baton Rouge.

 

Jami’an ‘yan sanda a Baton Rouge din suka ce guda daga cikin wanda ake zaton sun harbe ‘yan sandan ya rasu yayin da sauran guda biyu kuma suka tsere.

 

An dai harbe wadanan ‘yan sanda ne bayan da aka yi kiransu zuwa wani yanki da aka yi harbe-harbe. Yanzu haka dai jami’an tsaro sun bukaci mazauna wannan birni da su tallafa musu da bayanan da za su taimaka wajen kame wanda ake zargi da harbe ‘yan sandan.

Shi kuwa gwamnan jihar Louisiana John Bel Edwards ya ce jihar za ta yi amfani da dukannin karfinta wajen ganin an hukunta wanda ke da hannu a wannan aika-aika.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like