An Janye Dokar Hana Zirga-zirga Da Daddare A Jihar Borno


Gwamnatin jihar Borno ta cire dokar hana yawon dare ta makonnin uku wadda ke fara aiki daga Karfe goma da rabi na dare zuwa Karfe shida na safe.

Gwamnatin jihar dai ta kakaba dokar ce bisa bukatar da Kwamandan Rundunar Zaman Lafiya Dole, Manjo Janar Rogers Nicholas ya gabatarwa gwamnatin jihar don samun tabbatar da tsaro daga hare haren kunar bakin wake na kungiyar Boko Haram.

You may also like