An jiwo karar harbin bindiga a wurin zaben fidda gwani a jam’iyar APC na dan takarar gwamnan jihar Ekiti


An jiwo karar harbin bindiga a filin wasa na Olukayode dake Ado Ekiti babban birnin jihar Ekiti inda anan ake gudanar da babban zaben fitar da gwani na dantakarar da zai wa jam’iyar APC takara a zaben gwamnan jihar da za gudanar.

Baza a iya tabbatarwa ba ko harbin na jami’an tsarone ko kuma na yan bangar siyasa da suka kai harin wurin.

Yan takara 33 ne ke neman jam’iyar APC ta tsayar dasu takara,a zaben gwamnan jihar da za gudanar a watan Yuli.

Zaben yana cikin tafiya yadda yakamata cikin tsanaki kawai sai wani wakilin ya yi zargin cewa ana tafka magudi a zaben hakan ya sa aka shiga musayar yawu har ta rikici ya barke aka kuma dakatar da cigaba da zaben.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like