An Kaddamar Da Fara Tafsirin Mata A Jihar Bauchi


Uwargidan gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza Muhammad Abdullahi Abubakar ta halarci taron fara Tafisin watan Ramadan na Mata a jihar.


Taro wanda aka gudanar a babban dakin taro da ke gidan gwamnatin Neja jihar ya samu halartar mata da dama, daga ciki Uwargidan mataimakin gwamnan jihar Hajiya Fatima Nuhu Gidado ta samu halarta.

A wannan shekarar, Uwargidan gwamnan jihar ce ta dauki nauyin gudanar da Tafsirin.

Wannan ya fito ne daga Malam Shamsuddeen Lukman Abubakar, mataimaki na musamman ga gwamnan jhar kan Sadarwa.
©Zuma Times Huasa.

You may also like