An Kafa Kwamitin Riko Na Shugabancin APC A Gombe 



Kwamitin ayyuka na kasa na jam’iyyar APC ta sake sanya kwamitin mutum hudu da zasu jagoranci jam’iyyar a jihar Gombe.
Wannan yana kunshe ne a cikin wani takkadan manema labarai da kwamitin ayyukan na kasa ta fitar, ta hannun mai watsa labaran ta, Bolaji Abdullahi.
Takaddan tace jam’iyyar ta yi abunda ya dace ne a bisa dokan ta na sashi 13.1 (xvi da kuma xvii) bayan wa’adin kwamitin riko na jihar ya kare.
Sabbin wadanda aka saka a kwamitin sune kamar haka:
Idi Barde Gubana (Shugaba na jiha)
Sani Haruna (Mataimakin shugaba)
Bello Kasimu Maigari (sakatare)
Barr. Bichi Obadia (mai bada shawara fannin shari’a.)
Za’a rantsar da kwamitin ne a ranan Litinin, 20 ga watan da muke ciki a sakatariyar jam’iyyar dake Abuja.

You may also like