Mutane 7 ne suka mutu a harin bam da aka kai yankin Nangarhar na kasar Afghanistan.
Sanarwar da ma’aikatar ministan cikin gidan kasar Afghanistan ta fitar na nuna cewa, mutane 2 sun jikkata a harin da aka kai.
A yayin da hukumomin kasar ta sanarda cewa bam din an ajje kusa da hanya, a gefe guda kuma babu wanda ya dauki alhakin harin.
Kungiyar ta’adda ta Taliban da Daesh na yawan kai hare-hare a yankin Nangarhar.