An Kai Harin Kunar Bakin Wake A Maiduguri Wadansu ‘yan kunar bakin wake mata hudu sun kai hari a wajen birnin Maiduguri a arewa maso gabashin Najeriya, inda suka kashe kansu da kuma wani yaro.

Mutane da dama ne suka jikkata sakamakon harin wanda aka kai da safiyar ranar Asabar.
Biyu daga cikin ‘yan kunar bakin waken sun kai harin ne a kusa da wani barikin sojoji, inda suka kashe kansu.

Sauran biyun sun kai hari ne a wani kauye da ke Alakaramti wanda yake kusa da Maiduguri, inda su ma suka kashe kansu da kuma wani yaro.

Har ila yau harin ya jikkata wadansu mutum hudu, kamar yadda ‘yan sanda suka ce.

A cikin makon nan mutum 18 suka rasa rayukansu bayan wani harin kunar bakin wake a birnin.

Hare-haren suna zuwa ne duk da ikirarin da rundunar sojin kasar take yi na cewa tana samun nasara a yaki da Boko Haram.
Mezakuce?

You may also like