An Kai Sabbin Hare-Hare A Kudancin Kaduna


Rahotanni daga jihar Kaduna sun nuna cewa wasu mahara da ake zargi makiyaya ne sun kai wasu sabbin hare hare a kauyen Bakin Kogi a karamar hukumar Jema’a da ke jihar inda suka kashe akalla mutane hudu.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mukhtar Aliyu ya ce, an tura karin jami’an tsaro yankin don ganin an zakulo wadanda ke da hannu wajen kai harin. Haka ma, gwamnatin jihar Kaduna ta tura jami’an hukumar agajin gaggawa zuwa yankin sannan kuma ta jajantawa iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon harin.

You may also like