An Kai Sabon Hari A Jami’ar Maiduguri ‘Yan harin kunar bakin wake uku sun tarwatsa kansu da kansu a lokacin da suka yi kokarin kutsawa sashen ayyuka na jami’ar Maiduguri, jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya.
Harin ya auku ne da tsakar daren Asabar, kuma hukumomi sun tabbatar da cewa wani mai gadi na cikin wadanda suka mutu sakamakon fashewar bama-baman. Jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA da takwararta ta jihar Borno BOSEMA a Maiduguri sun kwashe gawawwakin.
Wadannan hare-hare na zuwa ne a lokacin da birnin Maiduguri ke fuskantar ƙaruwar masu yunkurin kai hare-haren kunar-bakin-wake, bayan jami’an tsaron kasar sun ce sun yi nasarar fatattakar mayakan Boko haram daga dajin Sambisa. Har yanzu dai babu cikakkun bayanai daga hukumomin tsaro da kuma na jami’ar Maiduguri game da wannan hari.

You may also like