
Asalin hoton, Inec
Hedikwatar Inec a Jihar Imo da aka ƙona a watan Disamba
Hukumar zaɓe a Najeriya ta ce an kai wa ofisoshinta hari a faɗin ƙasar sau 50 daga 2019 zuwa 2022.
A cewar bayanan da National Electoral Commission (Inec) ta fitar ranar Juma’a, hare-haren sun afku a jiha 15 jimilla, waɗanda suka haɗa da Imo (11), Osun (7), da Enugu (5), da Akwa Ibom (5), da Ebonyi (4), da Cross River (4), da kuma Abia (4).
Sauran su ne: Anambra (2), Taraba (2), Kaduna (1), Borno (1), Bayelsa (1), Ondo (1), Lagos (1), Ogun (1).
Shekarar 2020 ce shekarar da aka fi samun hare-haren inda aka kai sau 22, sai 2021 mai 12, da kuma 2019 da 2022 da aka kai hari sau takwas-takwas.
A farkon makon nan wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan hedikwatar Inec ɗin da ke Jihar Imo, wanda shi ne hari na uku da aka kai kan Inec ɗin cikin kwana 12 a jihar.
An fi samun hare-haren a jihohin kudu maso gabas, inda ƙabilar Igbo suka fi rinjaye, waɗanda hukumomi ke zargin mayaƙan ESN na ƙungiyar Ipob da ke neman kafa ƙasar Biafra da kaiwa.
Hukumar zaɓen ta ce tana da niyyar sauya wa wasu daga cikin matsugunanta mazauni a wuraren da take fama da irin waɗannan hare-hare.
A farkon nan ne Inec ta fara raba katin jefa ƙuri’a a ofisoshinta da ke ƙananan hukumomi ga mutum miliyan 93 da ta ce su ne suka yi rajistar zaɓe a faɗin ƙasar.
A ranar 25 ga watan Fabarairun 2023 ake sa ran fara kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen da ‘yan Najeriya za su zaɓi shugaban ƙasa da gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya da na jihohi.
Yadda aka kai hare-haren a jihohi
Asalin hoton, Inec
Hedikwatar Inec a Jihar Imo da aka ƙona a farkon watan Disamba
An kai hari sau huɗu a Jihar Akwa Ibom a 2019, biyu a Imo, da kuma ɗai-ɗai a jihohin Bayelsa da Osun.
A 2020, an kai hari biyar a Osun, huɗu a Cross River, huɗu a Imo, uku a Abiya, biyu a Taraba, ɗaya Anambra, ɗaya a Legas, ɗaya a Ondo, sai kuma ɗaya a Borno.
A 2021 kuma, hari uku aka samu a Ebonyi, uku a Enugu, biyu a Imo, ɗaya a Anambra, ɗaya a Abiya, ɗaya a Kaduna, da kuma ɗaya Akwa Ibom.
Bugu da ƙari, a 2022, an samu tashin hankali sau uku a Imo, biyu a Enugu, da kuma ɗai-ɗai a jihohin Ebonyi da Ogun da Osun.
Inec ta ce rahoton bai ƙunshi ƙonewar da ofisoshin suka yi ba sakamakon gobara da sauran haɗurra kamar ruwan sama da iska.