Zabukan da suka gabata a kasar da ta fi yawan jama’a a nahiyar Afirka, an yi fama da tashe-tashen hankula tsakanin magoya bayan jam’iyyun adawa, haka kuma an yi tashe-tashen hankulan siyasa da dama gabanin zaben ‘yan majalisar dokoki da na shugaban kasa da za a yi ranar 25 ga watan Fabrairu.
“Ba za mu iya ci gaba da amincewa da hare-haren da ake kai wa ‘yan adawar siyasa ba, wanda galibi ke kara ruruwa sakamakon kalaman tayar da hankali na shugabannin siyasa,” a cewar Obi a cikin wata sanarwa, inda ya bukaci ‘yan sanda su gudanar da bincike.
Nan take dai ba a bayyana ko su wanene ke da alhakin kai harin ba, amma gidajen talabijin na kasar sun nuna motoci da dama da aka lalata dauke da allunan jam’iyyar Labour da kuma wasu magoya bayan jam’iyyar da suka jikkata ana musu jinya a wurin gangamin yakin neman zaben da aka gudanar a cikin garin Legas.
Nan take dai ‘yan sandan yankin ba su ce komai ba.
A wajen gangamin, Obi ya shaida wa magoya bayansa cewa zai yi wa rundunar ‘yan sanda garambawul ta yadda zasu kara samun kwarewa, da kawo karshen satar man fetur da ke kawo cikas a harkar hakar mai a yankin Naija Delta, da kuma inganta tsaro domin bai wa manoma damar bunkasa harkokinsu.
Obi ne ke kan gaba a binciken jin ra’ayoyin jama’a da dama amma ana sa ran sakamakon zaben zai yi kusa-da-kusa. Matasa masu kada kuri’a, da suke jin bakin cikin tabarbarewar tattalin arziki, cin hanci da rashawa da rashin aikin yi, su ne manyan masu goyon bayan Obi.
Obi zai kara da Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar jam’iyyar APC mai mulki, da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP.