An kama ɓarawo na sata cikin  jirgin sama da ya tashi daga Abuja zuwa Lagos


Rundunar ƴan sandan Najeriya dake filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Lagos tatabbatar da kama wani da ake kira Kunle Oni, wanda ake zarginsa da aikata sata a cikin  jirgin da ya tashi daga Abuja zuwa Lagos.
Oni wanda sauran fasinjoji  suka kama shi yana sata a cikin jirgin saman kamfanin Air Peace da ya tashi daga Abuja zuwa Lagos.

Bandir din takardan kudin naira da ya sata daga jakar fasinjoji aka gano a jakarsa  bayan da jami’an tsaron fannin sufurin jiragen sama  suka yi masa tambayoyi lokacin da jirgin ya isa Lagos.

A  katin shedar da yayi amfani da shi wajen shiga jirgin ya nuna cewa yana aiki ne a wani kamfani da ake kira HB 

Da aka tambaye shi, lokacin da ya shafe yana sata a cikin jirgi sai ya kada baki yace,” wannan shekarar.”

Amma kuma ya buɗe jakar makaranta cike da bandir din kuɗi yan ₦1000  da ake zarginsa da ya sace su ne daga sauran abokanan tafiyarsa fasinjoji.

Bayan katin sheda na kamfanin HB da ake tunanin katin na bogine an kuma same shi da mallakar wasu katunan sheda na daban.

You may also like