Hukumar ‘yan sandan Nijeriya sun damke wani dan kasar Italiya mai suna Peter Nelson da ake zargin sa da halaka matarsa wadda mawakiya ce ‘yar kasar Nijeriya, mai suna Zainab Ali Nielson, wacce aka fi sani da Alizee, da kuma yar’ta mai shekaru hudu a duniya mai suna Petra.
An kashe su ne a gidansu dake Ocean Parade, Banana Island dake jihar Lagos a safiyar Alhamis din da ta gabata.
Duk da dai har yanzu babu cikakken bayanin dalilin yin kisan, amma majiyarmu ta tabbatar mana da cewa Peter yana tsare a hannun ‘yan sanda. Yayin da kuma gawarwakin suna mutuware domin binciken sanadin mutuwar tasu.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda ta jihar Legas SP Chike Oti, ya tabbatar da kama wanda ake zargi da laifin kisan, yace an tura kungiyar masu binciken gidan da aka aikata laifin.
Yace “kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Edgal Imohimi, ya bada damar damke wanda ake tuhuma, inda yanzu haka yana wurin ‘yan sanda.
Kwamishinan ya kara da cewa kungiyar binciken sun dauko duk wata shaida da suka samu domin yanke hukunci. Hukumar ta tura a rubuce zuwa ga ofishin jakadancin wanda ake zargin.