An kama gungun wasu masu garkuwa da mutane a jihar Abia


A wani abu dake kama da shirin fim, wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da Solomon Aniefiok, Kwamandan rundunar ƴan sandan kwantar da tarzoma na runduna ta 55 dake garin  Aba a jihar Abia 

Masu garkuwar riƙe da bindiga ƙirar AK-47 karkashin jagorancin, Ifeanyi Ekpelulor, sun kai wa kwamandan hari lokacin da yake cikin motarsa suna tattaunawa da mota a gefen titi.

Sun karɓi kuɗin diyar da ba a bayyana yawansu ba kafin su sake shi.

Jin haushin abin da yafaru yasa babban sifetan yan sanda Ibrahim Idris ya tura runduna ta musamman zuwa jihar Abia.

Rundunar ta samu nasarar kama mutane 5 cikin wadanda ake zargi da aikata laifin yayin da ɗaya ya mutu a musayar wuta.

Kayan da aka gano a wurin mutanen sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47, gidan harsashi guda biyu da kuma harsashi 60 sai kuma karamar bindiga mallakin kwamandan.

Sauran kayayyakin da aka gano sun haɗa da bindiga ƙirar gida guda ɗaya, rigar silke guda ɗaya, hular sanyi da sauransu.

 

You may also like