An Kama Jami’an Peace Corps 34 A Jihar Lagos 


Rundunar yan sandan jihar Lagos ta bada sanarwar kama jami’an kungiyar tabbatar da zaman lafiya wato Peace Corps su 34.

Olarinde Famous-Cole mai magana da yawun rundunar shine ya bayyana haka yace jami’an za a gurfanar dasu a  gaban wata kotun tafi da gidanka.

“Rundunar yan sandan jihar Lagos ta kama jami’an Peace Corps su 34,” yace. 

“Kungiyar ba halattaciya bace, saboda haka zamu gurfanar dasu a gaban kotun tafi da gidanka  a gobe.”

Famous-Cole yaki bayyana cikakken laifin da jami’an suka aikata da har takai ga an kama su.

Wannan dai wani koma bayane ga kungiyar da take neman shiga jerin sawun hukumomin tsaro dake kasarnan biyo bayan dokar da majalisar dattawa ta zartar  na amincewa da kungiyar ta shiga jerin sawun hukumomin tsaro na kasarnan.  

You may also like